World News in Dutch

Ya kashe diyarsa yar shekaru 4 har lahira

Yan sandan Jihar Akwa Ibom sun cafke wani mutum dan shekaru 30 mai suna Joseph Ibanga da laifin shake kashe yarsa mai shekaru 4 ta hanyar shake mata wuya.

Joseph Ibanga

Kamar yadda jaridar Nigeria Today ta ruwaito, a lokacin da yan sanda ke masa tambayoyi Ibanga ya amsa laifin kashe diyar tasa biyo bayan cin abincin da mahaifiyarsa ta girka.

Yace: “ni mazunin fatakwal ne, ban san abin da ya faru wata rana da nazo kauye sai muka dinga cacar baki da mahaifiyata. Daga nan sai naji wani abu a jikina yana cemin in kashe yata dake kwance tana barci. Da karfe 4 na asuba ne a kaita bakin rafi na shake mata wuya.

Ibanga ya kara da cewa “shi kan shi bai san dalilin da yasa ya aikata wannan aika aikan ba, don sai bayan na kashe yarinyar ne hankalina ya dawo jikina. Daga nan ne fa na gane tabbas na aikata mummunar laifi. Da na dawo gida sai mahaifiyata ta tambayeni ina yarinyar.

Toh dana kasa yi mata gamsashshen bayani ne dai ta kwala ihu tana kiran makwabtan mu, daga nan kuma yansanda suka kamani, ban san abin da yasa na aikata hakan ba, nayi da na sani.”

The post Ya kashe diyarsa yar shekaru 4 har lahira appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

Читайте на сайте