World News in Dutch

EFCC ta damke dan majalisar tarayya

-Hukumar EFCC ta kama wani dan majalisar tarayya daga jihar Akwa Ibom mai suna Nse Bassey Ekpenyong

-An kama shi da zargin mallakar takardar shedar karatu ta jabu

-An bada belin dan majalisar yayin da aka ci gaba da bincike

Rohoton Sahara Reporters na cewa wata kungiya mai zaman kanta ta zargi Ekpenyong wajen hukumar hana cin hanci da rashawa akan yin karya da almundahana

Kungiyar mai zaman kanta ta zarge shi da bada takardar kammala karatun karamar diploma daga polytechnic ta jihar Abia ga hukumar zabe ta kasa yayin da ake kusa da yin zaben ‘yan majalisar tarayya na 2015.

KU KARANTA : EFCC ta kama wani dan majalisar wakillai

An zarge shi da amsar alawus da wasu kudade a kan takardar jabu da ya bada, kuma binciken da hukumar EFCC tayi ya nuna cewa Ekpenyong bai halarci makarantar ba, kuma takardar shedar da ya bada ba daga makarantar ta fito ba

An dai bada belin sa yayin da aka ci gaba da bincike

The post EFCC ta damke dan majalisar tarayya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

Читайте на сайте