Majalisar tayi Allah wadai da kokarin cire Saraki
-Majalisar Dattawa ta zargi bangaren zartaswa da kokarin cire Saraki da Ekweremadu
-Ministan shari’a da kuma wasu shuwagabannin jam’iyya ba kokarin cire Saraki da Ekweremadu saboda dalilai Na son Zuciya.
ike Ekweremadu da bukola saraki
Majalisar dattawa ta zargi bangaren zartaswa na gwamnatin tarayya da kokarin murkushe bangaren dokoki domin a samesu da laifin da zai sa a canza shuwagabannin su.
KU KARANTA: Ofishin ‘yan sanda ta gayyaci David Mark da Ekweremadu
Sanata Aliyu Sani Abdullahi, shugaban kwamitin sadarwa da huddar jama’a wanda yayi magana da yawun Majalisar yace shirin tuhumtar shugaban majalisar dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki, da mukaddashinsa Ike Ekweremadu, da akawun majalisa Mai barin gado Alhaji Salisu Maikasuwa da mukaddashinsa Mr. Ben Efeturi da zargin yin takardar jabu ta dokokin zaben a majalisa zai maida kasar cikin halin rashin sanin yakamata da aiki da doka wadanda mukayi watsi da su. Ya cigaba da cewa
“Dole ne mu fito karara mu nuna ma mutanen da ke bangaren zartaswa, da shuwagabannin jam’iyya dake bayan kokarin cire shuwagabanninsu cewa durkusama wada ba gajiya wa bane. Majalisar tayi iya kokarinta na nuna dattako ga shugaban kasa.
“Akwai lokutta da bangaren zartaswa ya kauce hanya,amma muka kauda kai domin ci gaban kasa, da kuma ganin irin halin da kasar take ciki na matsin tattalin arzikin kasa”.
Ya ci gaba da cewa,
“Wannan sabon shirin na ganin a canza shuwagabannin majalisar ta hanyar tozarta su zai maida hannun agogo baya”.
The post Majalisar tayi Allah wadai da kokarin cire Saraki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.