Dalilan da yasa ba zamu daina jefa bama-bamai a dajin Sambibsa ba – Hukumar sojoji

– Helkwatan tsaro tace ta dogara kan makamai masu zama wajen hare-harenta a dajin Sambisa

– Kakakin hukumar tsaro Birgediya Janar Rabe Abhbakar yace an nakasa Boko Haram da farmakin da ake kai ma ‘yan ta’addan

– Abubakar yace zasu fara aikinsu mai suna SHARANDAJI domin takaita satar shanu Wanda zai rage rashin jituwa tsakanin makiyaya da manoma

Helkwatan tsaro tace sojojin Najeriya zasu ci gaba da jefa bama-bamai a maboyar Boko Haram a dajin Sambisa duk da sakin yaran Chibok 21 da aka yi da kuma kokarin da ake yi na sako sauran ‘yan matan.

KU KARANTA: Labari da duminsa: Kotu ta yanke hukunci kan karar Olisa Metuh

Mai rikon matsayin kakakin hukumar tsaro, Birgediya Janar Rabe Abubakar ya fada ma The Sun cewa sojoji zasu dogara kan makamai masu zama domin kauce ma asarar rayukan farar hula. Janar Abubakar ya ci gaba da cewa, an nakasa Boko Haram, kuma bata rike da wani bangare na kasar nan komin kankartarsa.

The post Dalilan da yasa ba zamu daina jefa bama-bamai a dajin Sambibsa ba – Hukumar sojoji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте