Labari da dumi: Buhari ya bada umarnin bincikar Abba Kyari
Wani rahoto na karkashin kasa ya labarto mana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sashin bincike na musamman na hukumar yansanda dasu binciki shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Alhaji Abba Kyari kan zargin karban cin hanci da ake yi masa.
Buhari da Abba Kyari
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewar da alama binciken baya rasa nasaba da kudaden da ake zargin kamfanin MTN ta baiwa Abba Kyarin da suka kai naira miliyan 500 don ya sanya baki gwamnati ta rage mata tarar dala biliyan 5 da aka yanke mata.
Majiyar tamu data bukaci a sakaya sunanta tace “jami’an kamfanin MTN da aka gayyace su don amsa tambayoyi game da zargin sun musanta batun cewa sun biya wasu kudade ga wani tun da aka fara maganan sanya tarar na dala biliyan 5, kuma babu wanda ya nemu su bashi ko sisi. “karin bayani ma shi ne idan da an biya irin wannan makudan kudade ta hanyar bakuna, toh da hukumomin tsaro sun gano hakan.”
KU KARANTA: Ya musulunta saboda ya auri budurwarsa musulma
Idan ba’a manta ba, hukumar kula da kamfunan sadarwa na Najeriya ce ta maka ma kamfanin MTN tarar dala biliyan 5 saboda kin kulle layukan da suka ki yin rajista da yawansu ya kai dubu 100. Jaridar Sahara Reporters ne ta dauko rahoton cewa MTN ta biya Abba Kyari naira miliyan 500 don yayi amfani da kusancinsa da shugaba Buhari ya nema masu sauki.
Wannan batu yazo ne daidai lokacin da MTN din tayi tayi a rage mata kudaden tarar, inda ta dinga shiga kotuna daban daban, har ma da yin amfani da jakadun kasa da kasa, amma hakan ta bai cimma ruwa ba.
Sakamakon nauyin zarge zargen ne yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari umartar babban hafsan jami’an yansanda Ibrahim Idris ya binciki Abba Kyari don gano gaskiyar lamarin.
The post Labari da dumi: Buhari ya bada umarnin bincikar Abba Kyari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.