Wata kungiya ta karrama Gwamna Masari saboda wannan daliban

Wata kungiya mai suna ‘Think Nigeria First Initiatibe (TNFI)’ mai zaman kanta, wacce kuma ta kware wajen gyara halayya da wayar da kan jama’a da kuma koyar da dabi’u na kwarai, ta yaba wa Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari bisa ci gaban da ya kawo a fannin ilmi a jihar.

Masari tare da Shugaba Buhari

Babban Darakta Janar na kungiyar, Ambasada Abubakar Tsanni ne ya yi yabon a lokacin da suka kai ziyarar ban girma ga Gwamna a gidan gwamnati da ke Katsina.

A cewar Ambasadan, duk da matsalar tattalin arzikin kasar nan, Gwamna Aminu Masari ya yi nasarar gyara makarantun Firamare da na Sakandare guda dubu daya, sannan ya gina wasu sabbi guda ashirin da shida a fadin jihar, duk a cikin shekara daya kacal.

KU KARANTA KUMA: An sake makudan kudade a mulkin Jonathan

A cewarsa, a yayin da wasu jihohi ke murnar an gyara masu rufin makarantu,amma a jihar Katsina kuma mutane na murnar gyaran dukkan makarantu ne, domin a yanzu haka kusan dukkan makarantun Katsina an gyarasu, sannan kuma ga kayan karatu da kyautata wa ma’aikata da ake yi.

Ya ce, “gaskiya Gwama Matsari ya ciri tuta, domin babu abin da yake tunani a ransa illa ci gaban Katsina. Muna yaba wa jihar katsina a bisa rawar gani da ta taka a jarabawar karshe ta ’yan Sakandare, wato WAEC a shekarar 2016, ind jihar ta zo ta biyu a duk fadin kasar nan, sannan ta zo ta daya a duk fadin jihohin Arewacin kasar nan.”

Ambasadan ya ci gaba da bayyana cewa, “nasarar da aka samu a fannin jarabawar WAEC alama ce da ke nuna irin ci gaban da aka samu a fannin ilimi a karkashin mulkin Gwamna Masari. An samu ci gaba a fannin Malamai da dalibai da kuma kula da makarantu, wanda wannan na taimakawa wajen ci gaban fannin ilimi. Nasarar da Gwamna Aminu Masari ya samu a cikin shekara daya a fannin ilimi ba a taba samun irinsa ba a tarihin jihar Katsina.

Daga nan sai Ambasada Tsanni ya bayyana cewa kungiyar tasu za ta bayar da tata gudumawar wajen bunkasa ilimi a jihar, inda ya ce dukkan Kananan Hukumomin jihar za su sami takardun rubutu 5,000 da sauran wasu kayan karatu, inda jihar Katsina kawai za ta samu jimlar takardu 170,000.

KU KARANTA KUMA: Hukumar kwastam ta sallami wasu ma’aikatanta

Cikin tawagar da suka ziyarci Gwamna, akwai Shugaban Majalisar Dokoki ta Katsina, Hon. Aliyu Sabi’u  Muduru da sauran ’yan kungiyar, inda suka kai ziyarar gani da ido zuwa wasu makarantun da aka gyara a jihar.Wasu daga cikin makarantun da suka ziyarta, sun hada da Kwalejin gwamnati da ke  Ajiwa, da Kwalejin gwamnati ta Kaita da dai sauransu.

The post Wata kungiya ta karrama Gwamna Masari saboda wannan daliban appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте