Gwamnonin arewa sun gana da John Kerry
– Gwamnoni 10 cikin gwamnoni 19 na arewacin Najeriya sun gana da da sakataren wajen Amurka a ranan laraba,19 ga watan oktoba a Washington DC
– Kana sun gana da mai baiwa shugaba Obama shawara akan tsaro Ambasada Susan Rice
– Ganawar sun tattauna ne akan hadaka akan magance rigingimun addini da kabila da ke faruwa a arewacin Najeriya
Gwamnoni 10 cikin gwamnoni 19 na arewacin Najeriya sun gana da da sakataren wajen Amurka a ranan laraba,19 ga watan oktoba a Washington DC
Gwamnonin arewa karkashin jagorancin gwamnan jihar Barno sun tattauna ne akan magance rigingimun addini da kabila da ke faruwa a arewacin Najeriya.
KU KARANTA: Mabiya nagari: Matsalar Najeriya
Gwamnonin da suka halarta sun hada da, Darius Ishaku na jihar Taraba, Dalong na jihar Plateau, Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara, AbdulAziz Yari na jihar Zamfara, Bindo Jibrilla na jihar Adamawa, Muhammad Abdullahi Abubakar na jihar Bauchi, Abubakar Sani Bello na jihar Niger, Kashim Shettima na jihar Borno, Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto da maaimakin jihar Kano, Professor Hafiz Abubakar wanda yake wakiltar gwamnan jihar Kano.
The post Gwamnonin arewa sun gana da John Kerry appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.