Yawan kudaden da aka sace cikin shekaru 7 a mulkin Jonathan zai baka mamaki (Karanta)

Mukarraban gwamnati Mutane 55 Ne Suka wawure Naira Tiriliyan 1.3 Daga Asusun Kasa A Cikin Shekaru Bakwai Na Gwamnatin Jonathan, Kamar Yadda Kwamaitin Bada Shawarwari Kan Rashawa Na Fadar Shugaban Kasa (PACAC) Ya Bayyana.

Tsohon Shugaban kasa Goodluck jonathan

Shugaban kwamitin ba fadar shugaban kasa shawara a kan yaki da cin hanci da rashawa, Itse Sagay ya kuma bayyana cewa da ba shugaban kasa Buhari ba shi ke kan shuganan cin kasar nan a yanzun ba da tuni kasar ta zo karshe.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Majalisar Dinkin Duniya ta yaba wa Buhari

“da Buhari bai zo ba, ba na tunanin da har yanzun akwai wata kasa Nijeriya” Da sai kasar Zimbabwe ta fi Nijeriya inji Mr Sagay.

Sai dai dinbi masu maida martani a kafar da muka samo labarin ta Premium Times, dumbin masu mayar da musayar ra’ayi na ta sukar lamirin maganar ta Mr Itse Sagay, inda suke cewa a ciki maganar tasa ya mance Allah ya sa shugaba Buhari a matsayin danda ya tsare kasar ba Allah ba.

A wani labarin kuma Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yaba da irin muhimmiyar rawar da kasashen kasa da kasa irin kungiyar bada agaji ta Red Cross da wasu kasashe suka taka wajen sako wasu ‘yan matan Chibok 21 cikin wadanda aka sace fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Yayinda yake ganawa da Mr. Peter Maurer shugaban kungiyar Red Cross a fadarsa dake Abuja yau Litinin, shugaba Muhammad Buhari yace gwamnatinsa ashirye take ta cigaba da tattaunawa da kungiyar Boko Haram “muddin ta yarda da shiga tsakanin kungiyoyi irinsu Red Cross.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta kwato makudan kudade daga jihar Borno

Yace “Munga sakamakon tattaunawar da muka yi kwana kwanan nan gashi ‘yan matan Chibok 21 sun dawo”, inji shugaban yayinda yake misali da irin rawar da kungiyar Red Cross ta taka wajen ba ‘yan matan taimakon jin kai a matakin farko. ‘Kada a manta ‘yan matan sun kwashe kwanaki 900 a hannun wadanda suka sacesu.

The post Yawan kudaden da aka sace cikin shekaru 7 a mulkin Jonathan zai baka mamaki (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте