Ronaldo ya kafa wannan muhimmin tarihin (Karanta)

– Kwallo uku da Cristiano Ronaldo ya zura shi kadai a karo na 39 sun bai wa Real Madrid karin damar ci gaba da zama ta daya a saman tebirin gasar La Liga bayan sun doke Atletico da ci 3-0

– Dan wasan gaban na Portugal ya soma zura kwallo ne bayan an jefo kwallo daga bugun firi-kik inda ya bai wa golan Atletico Jan Oblak kafa

Ronaldo and Zidane

Ronaldo ya kara kwallo ta biyu daga wurin bugun fenareti, inda kuma ya cike kwallo ta uku bayan ya samu kwallon da Gareth Bale ya mika masa.

KU KARANTA: Tinubu da mukarrabansa sun kauracewa gangamin APC

Yanzu dai Real suna kan gaban Barcelona, wacce ita ce ta biyu, da maki hudu bayan da suka tashi babu ci a wasan da suka yi da Malaga.

Ronaldo ya zura kwallo takwas a gasar La Liga ta bana, inda ya yi kankankan da Lionel Messi da Luis Suarez.

Kwallo ukun da dan wasan mai shekara 31 ya zura sun sa ya fi shahararren dan wasan Real din nan Alfredo Di Stefano, wanda ya zura ci 17, yawan kwallaye da guda daya a wasannin da Madrid ta fafata.

A wani labarin kuma, Chelsea ta karbe jagorancin teburin Premier bayan da ta bi Middlesbrough har gida ta doke ta da ci 1-0, a wasan mako na 12 na gasar ta Premier.

Diego Costa ne ya ci wa Chelsea kwallon a minti na 41 da wasa, kuma dan wasan ya kasance jigo wajen kai hare-hare a wasan a bangaren Chelsea.

Wannan shi ne karo na farko da Middlesbrough ta yi rashin nasara a cikin wasanni hudu da ta yi.

Yanzu Chelsea ta tsallako da maki 28 ta wuce Liverpool wadda kafin wasan ita ce ta daya, da kuma Manchester City ta biyu, masu maki 27 kowacce, yayin da Boro take ta 15 da maki 11, mataki daya tsakaninta da faduwa daga tebur.

The post Ronaldo ya kafa wannan muhimmin tarihin (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте