Yanzu haka: Shugaban ma’aikatar tsaro yayi shellar mutane 50 da ake nema kan Boko Haram (hoto)

Shugaban ma’aikatar tsaro, Manjo-Janar Abayomi Gabriel Olonishakin ya bayyana manyan mayakan Boko Haram 50 da ake nema.

Ana neman wadannan yan Boko Haram din ruwa a jallo

Wannan kari ne ga wadanda aka yi shellan nema a baya. A watan Oktoba na shekara ta 2015, shugaban hafsan soji Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi shellar mambobin kungiyar ta’adda na Boko Haram guda 100 da ake nema.

Olonishakin, a cewar jaridar Daily Trust, yayi shellar ne a ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba a gurin wani taro da akayi a Theater Op Command a Maiduguri, jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Fulani makiyaya sun kai hari a Abuja

Shugaban hukumar tsaron ya bukaci jama’a da su samar da bayanai masu amfani da zai iya taimakawa rundunar soji guri kama wadanda ake zargin kuma suyi nasarar yaki da ta’addanci.

Jihar Borno na daga cikin jihohin Najeriya mafi girma da abun ya shafa wanda yayi sanadiyar halaka garuruwa da dama.

Olonishakin yace shellar neman su ya taimaka a baya ya kuma ce ya tabbatar wannan zai yi aiki don ceto kasar daga hannun yan ta’adda.

The post Yanzu haka: Shugaban ma’aikatar tsaro yayi shellar mutane 50 da ake nema kan Boko Haram (hoto) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте