Mun ci karfin yan Boko Haram, saura karasawa – inji sojojin Najeriya
– A Najeriya, rundunar sojin kasar ta musanta cewa ta rage yawan sojojinta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno
– Rundunar sojin na mayar da martani ne akan fargabar da wasu mazauna birnin Maiduguri ke yi cewa, karuwar hare-haren kunar bakin wake daga ‘yan kungiyar Boko Haram yasa gwiwar su ta yi sanyi
A wata hira da majiyar mu tayi da wasu mazauna birnin Maiduguri sun bayyana cewa matakin rage sojojin ya taimaka wajen karuwar hare-hare kunar bakin wake da ake fuskanta a jihar tare da haifar da fargaba.
KU KARANTA: Kasar Amurka ta soki Najeriya game da muzgunawa yan Shi’a
Sai dai kakakin rundunar sojin kasa ta Nigeria Kanar Sani Usman Kukah Sheka ya ce bai kamata ba wasu jama’a su rika cewa ana cikin fargaba a birnin Maiduguri, inda ya nanata cewa sojojin kasar sun karya lagon Boko Haram.
A wani labari makamancin wannan kuma, Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun dakile wani yunkuri na kai harin kunar bakin wake a sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
An yi yunkurin kai harin ne kwana daya, bayan wasu ‘yan kunar bakin wake da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hare-hare a birnin, ciki har da kofar shiga sansanin na Bakassi.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriyar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya ce dakarun rundunar Operation Lafiya Dole dake Maiduguri sun harbe wani dan kunar bakin wake da safiyar Lahadi, yayin da yake kokarin kutsawa cikin sansanin ‘yan gudun hijiran na Bakassi.
Kanar Kukasheka ya ce bayan an harbe dan kunar bakin waken, jami’ai tsaro masu kwance bom sun lalata bom din dake jikinsa kafin ya kai ga tashi.
Hare-haren kunar bakin wake na neman dawowa a birnin na Maiduguri, bayan an samu saukin hare-haren na lokaci mai tsawo.
The post Mun ci karfin yan Boko Haram, saura karasawa – inji sojojin Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.