YANZU-YANZU: FG ta gurfanar da alakalin kotun koli Ngwuta

Ngwuta ya bayyana gaban mai shari’a John Tsoho kan zargin laifuffuka 16.

Justice Ngwuta

An gurfanar da alkalin kotun koli mai shari’a Sylvester Ngwuta gaban wata babbar kotun kasa dake Abuja ranar Litinin 21 ga Nuwamba.

Ngwuta ya bayyana gaban mai shari’a John Tsoho kan zargin laifuffuka 16 da ake masa wadanda suka kumshi halarta haramtattun kudade da kuma karbar cin hanci wadanda gwamnatin tarayya ke masa. Ya musanta duk zargin da ake masa.

KU KARANTA: Wata budurwa ta saka kayan aure a ranar auren saurayin ta

A cikin zargin da ake masa, ance Ngwuta ya bayar da kudi N505m “wadanda suke cikin naira da dalar Amurka” ga wani dan kwangilar gine-gine mai suna Nwamba Linus Chukwuebuka tsakanin Janairu da Mayu 2016. Ana kuma zargin Ngwuta da ajiye makudan kudade wadanda suka hada da kudaden kasashen waje wadanda ake zargin ya same su ta haramtattun hanyoyi, abinda ya saba ma dokar hana halarta haramtattun kudade. Ana kuma zargin Ngwuta da laifin mallakar paspo na shigi da fici a sabbin zarge-zargen da ake masa.

Ngwuta na daya daga cikin alkalan da aka kama sanadiyar samamen da jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka kai gidajen alakalan manyan kotuna har dana kotun koli a kasar baki daya wasu makwanni da suka wuce.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

The post YANZU-YANZU: FG ta gurfanar da alakalin kotun koli Ngwuta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте