Ana ci gaba da farutar Zabiya a Tanzania
Kamar sauran mutanen Afirka, wasu daga jama’ar Tanzania tsafi da camfi na da matukar muhimmanci a rayuwarsu, kama daga gama garin ‘yan kasa zuwa ‘yan siyasa, da manyan ‘yan kasuwa, yawancin su sun yi imani da tsafi da camfa zabiya
Zabiya wata cuta ce da rashin sinadarin da ke bawa jiki launi ke sabbaba ta, kuma a cikin ko wane mutum 1,400 na Tanzania guda 1 zabiya ne; adadin da ya zarce na duniya baki daya inda duk cikin mutune 20,000 ne a ke samun zabiya 1 a duniya.
A cewar masana, yawan zabiyan na faruwa ne sanadiyyar takaice auratayya cikin kabila daya. Farautar zabiya ta zamar wa mutane jiki su na ganin cewa ruhin zabiya ba ya mutuwa, kuma su na kawo Sa’a. A cewar wani mai bincike, Giorgio Brocco: “Mutanen da ke da cutar zabiya na fuskantar muzgunawa a Afirka sannan a na ganinsu kamar wasu ‘yan baiwa.”
Hukumar adalci da zaman lafiya ta Tanzania ta yi nuni da cewa, “yawancin mutane sun yi imani zabiya na da wani tasiri wajen tsafi, kuma su na iya maida mutane masu kudi.”
A Tanzania da yawa daga mutane su na ganin sassan jikin zabiya su na da tasiri wajen tsafi kuma su kan yi amfani da sassan jikin don yi layu na samun sa’a a kasuwanci da siyasa. Wannan yanayi ya jawo mummunar dabi’ar farauta, da azabtarwa, da kuma kashe bil’adama. Wannan ya tabbatar da cewa ‘yan siyasa da masu hannu da shuni su na kashe zabiya.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 25 a garuruwa 3 a Zamfara
A kasar Tanzania wadda kudaden shigarta a shekarar 2010 ya ke dala miliyan 442, a cewar wakilin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijira, farashin hannu ko kafa ka iya kaiwa Euro dubu 3, gangar jiki gaba daya kuma na kaiwa Euro 60000. A kan yi farautar yara ta hanyar amfani da adduna.
A cewar masu wayar da kan al’umma, daga shekarar 2006 an kashe zabiya guda 71, an kuma afkawa 29 amma tuhuma goma ne a ka iya gabatarwa a gaban kotu. A kalla zabiya 10,000 ne a ka tilastawa guduwa daga mazaunansu. Tare da cewa gwamnatin Tanzania ta haramta tsafi tun watan Janairun shekarar 2016, kuma a na ta kamfe don hana wannan rashin imani, har yanzu wasu ‘yan siyasar na amfani da tsafi yayin gudanar da yakin neman zabe don samun nasara kan abokan hamayyarsu. Kasancewar hokumomi sun fara bada kariya ga zabiya, diloli su na ganin ya kamata farashin tsafi ya daga.
Ku biyo mu shafinmu na Tuwita a @naijcomhausa
The post Ana ci gaba da farutar Zabiya a Tanzania appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.