EFCC na farautar ‘yaruwar Fayose kan wani gida mai darajar N200 miliyan

– Takardun EFCC dake kotu na nuna cewa wani katafaren gida dake Abuja mai sunan uwargida Moji Ladeji na Fayose ne

– Hukumar hana cin hancin tace yana son badda sawu ne

– Ana son yaruwar Fayose tayi bayanin alakarta da maganar

Jami’an hukumar EFCC

Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fara farautar uwargida Moji Ladeji, yaruwa ga gwamna Ayodele Fayose kan gidan N200 miliyan dake lamba 44 a Osun crescent, Maitama Abuja.

KU KARANTA: Tofa! Mazabar Abdulmuminu Jibrin ta maka majalisar wakilai kotu

A cewar Sahara Reporters, ana zargin Ayodele Fayose da sayen gidan da kudaden rashawa amma takardun mallakar gidan na nuna cewa na yaruwar Fayose ne. Takardun da EFCC ta baiwa kotu na nuna cewa Fayose yayi haka ne domin ya barda sawunsa. Wata majiya a EFCC na cewa duk da yake yaruwar Fayosen na zaune a Britaniya, dole ne ta bayyana a EFCC domin yin bayani.

Ana dai zargin Ayodele Fayose da hannu cikin almundahanar $2.1 biliyan ta sayen makamai daga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

The post EFCC na farautar ‘yaruwar Fayose kan wani gida mai darajar N200 miliyan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте