Fayose ya gargadi ‘yan Ghana game da zaben kasarsu

– Mutanen Ghana zasu yi zaben shugaban kasarsu ranar 7 ga Disamba kuma gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yayi masu gargadi game da zaben tumun dare

– Gwamnan mai kawo kace-nace yace bai kamata ‘yan Ghana su dauki jam’iyya mai ikrarin ‘canji’ da gaske ba kamar yadda ‘yan Naneriya suka yi cikin 2015

Nigeria vs Ghana

Gabannin zaben shugaban kasa da za’a yi a Ghana ranar 7 ga Disamba, gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya gargadi kasar da kada suyi kuskuren da ‘yan Najeriya suka yi a zaben shugaban kasa na 2015.

A cewar Fayose, kuskuren da ‘yan Najeriya suka yi shine na zaben canji abinda ya jaza yunwa, kunci da tabarbarewar tattalin arziki a kasar yadda har kasashen dake sashen Afrika ta yamma abin na shafarsu.

KU KARANTA: Tofa! Mazabar Abdulmuminu Jibrin ta maka majalisar wakilai kotu

A wani jawabj daga kakakinsa Lere Olayinka, Fayose yace: “Dalilin amincewa da sakon All Progressive Congress (APC) na canji, yanzu ‘yan Najeriya na fuskantar yunwa da wahalar da ba’a taba ganin irinta ba cikin shekaru 30 da suka wuce, kuma bai kamata mutanen Ghana su fada cikin irin wannan tarkon ba.”  Sanafwar wada NAIJ.com ta samo tace gwamnan yayi wannan kiran yayin da yake amsar bakuntakar wasu malaman addini daga Ghana ranar Assabar 19 da Nuwamba.

“Bai kamata mutanen Ghana su amince da yaudara ta jam’iyyar adawa ba dake kiran a canza gwamnati. Mamadin haka, kamata yayi su maido shugaba mai ci John Mahama wanda yayi rawar ganin daya cancanta a sake zabensa. Ya kamata ‘yan Ghana su gane cewa a Najeriya canji shi ya kawo mana yunwa, kunci da rashin bin doka da kuma kama ‘yan Najeriya da tsare su ba tare da shari’a ba, kuma kuyi hattara da masu ikrarin canji gareku.”

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

The post Fayose ya gargadi ‘yan Ghana game da zaben kasarsu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте