Mazauna Jos sun tsorata game da labarin shinkafar jabu
Masu saida shinkafar na kukan rashin ciniki.
Har yanzu babu wata hukumar data tabbatar da labarin dake bazuwa cewa China na shigowa da shinkafar roba.
Duk da haka abin ya jawo storo da firgita ga jama’a balle ma a Jos babban birnin jihar Plateau. Daily Trust ta ruwaito cewa mutane kan tambayi masu saidawa shedar cewa shinkafarsu ta gaskiya ce.
KU KARANTA: Yanzu haka: Shugaban ma’aikatar tsaro yayi shellar mutane 50 da ake nema kan Boko Haram (hoto)
Masu saida shinkafar na kukan rashin ciniki. Ta bakin wata mai sayen shinkafa a wani shago dake Bukuru wani babban wurin hada-hada dake kusa da Jos wadda tace: “So muke mu tabbatar cewa ba shinkafar roba bace zamu saya mu kaima iyalinmu, mun karanta rohotannin dake gargadi game da shinkafar roba dake kasuwa, ya kamata muyi hattara.”
Mai sayen shinkafar wadda bata son a fadi sunanta tace ta sami labarin daga makwabta da ‘yan uwa wadanda suka gaya mata cewa sai sun yi gwaji tukum kafin su saya domin tabbatarwa. Tace ita ma ta binciki rohoton domin yima jama’a gargadi don kada su sayi roba mamadin abinci.
Ita ma ta baza labarin inda tace: “Ni ma na baza labarin domin in taimaki wasu, ni dai ban karanta wani rohoto game da asalin wannan labarin ba a duk rohotannin dana karanta.”
Wani babban dan kasuwar shinkafa dake Jos yace ya kwashi kwanaki biyar yana jawo hankalin masu saye domin su saya wajensa, amma duk da haka bai yi ciniki mai yawa ba.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Mazauna Jos sun tsorata game da labarin shinkafar jabu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.