Assha: An kama Fasto yayi fyade
– ‘Yan Sanda sun kama wani Fasto da laifin yi wa wata fyade a Jihar Bayelsa
– Ana zargin wannan Fasto mai shekaru 38 da wasu mutane da laifin fyade
– Shekarar Yarinyar da aka aikata wannan abin assha da ita 11
Wani abin kunya ya faru a Garin Bayelsa, inda aka kama wani Fasto da laifin yi wa wata karamar yarinya fayde. Duka-duka dai yarinyar ba ta wuce shekaru 11 a duniya ba. Wannana abu dai ya faru ne a Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu.
Bayan Faston, ‘Yan Sanda sun kuma kama wasu mutane 6 dabam da suka yi wannan lalata. Ana dai zargin su da aikata fyade da yara ‘Yan shekara 11 da kuma wata mai shekaru 2 kacal a duniya.
KU KARANTA: An kai hari Gidan Mamman Daura
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, Mista Adeyemi Ogunjemilusi ya tabbatar da hakan a Birnin Yenagoa. Bayan wadannan kuma an kama wani matashi kafinta da yayi fyade ga wata kuma ‘yar shekara 8. Kafinta yayi wannan aika-aika ne a shagon aikin sa.
A baya dai an samu wata Yarinya mai suna Lekhula, da ta bayyana yadda wani limamin coci ya yaudare ta, Fasto Attie Kgware ne yayi mata alkawarin mota, ya kwanta da ita. Lekhula ta bayyana cewa Faston bai ko yi amfani da bororon roba ba, ya fada mata cewa yafi tsarki a hakan. Tuni dai ya zuba mata ciki ya kuma ce fau-fau ba shi ba ta.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Assha: An kama Fasto yayi fyade appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.